Afcon

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 6

Za a buga wasa na uku da na huu a zagaye na biyu ranar Lahadi a gasar cin kofin nahiyar Afirka da Morocco ke karɓar baƙunci.

Wasa ne tsakanin mai masaukin baƙi, Morocco da Tanzaniya da kuma na hamayya tsakanin Afirka ta Kudu da Kamaru da za a kece raini.

Moroocco ta taɓa lashe Afcon a 1976, Afirka ta Kudu tana da ɗaya da ta ɗauka a 1996 da Kamaru mai biyar (1984 da 1988 da 2000 da 2002 da kuma 2017), yayin da Tanzaniya ke fata.

Senegal ta zama ta farko da ta kai zagayen kwata fainal a Afcon, bayan da ta doke Sudan 3-1 ranar Asabar, karo na tara da ta kai wannan matakin a tarihi.

Ta kuma yi karawa 15 a jere ba tare da rashin nasara ba a Afcon da cin wasa 10 da canjaras biyar daga ciki.

Source link